25 Nuwamba 2025 - 08:15
Source: ABNA24
Iran Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Isra'ila Ta Kai A Yankin Kudancin Beirut

Ofishin Jakadancin Iran a Lebanon ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin harin "matsorata" da gwamnatin sahyoniya ta kai a yankin kudancin Beirut a gundumar Dahiyeh.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa: Ofishin Jakadancin Iran a Lebanon ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin harin "matsorata" da gwamnatin sahyoniya ta kai a yankin kudancin Beirut a gundumar Dahiyeh.

A cewar IRNA, a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin X a ranar Lahadi, ofishin jakadancin ya ce, "Yanzu laifuka da ayyukan ta'addanci da [gwamnatin sahyoniya] ta aikata sun fadada har zuwa yankunan kudancin Beirut. Wannan yana dauke da alamar samuwar 'yan ta'addan Isra'ila, wacce kuma ba ta nuna wata shakka ba wajen sanya fararen hula marasa laifi na kasar Lebanon cikin hadari".

Jawabin ya kara da cewa, "Waɗannan hare-haren ta'addanci ba za su taba karya muradun ma’abuta gaskiya ba kuma ba za su raunana kudurinsu na kin amincewa da zalunci ba".

A safiyar yau, gwamnatin sahyoniyawa ta ci gaba da kai hare-haren sama a Lebanon, inda ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai wani sabon hari ta sama a yankunan kudancin Beirut.

A cewar rahotannin farko, mutane biyar sun yi shahada yayin da wasu ashirin suka jikkata a harin ranar Lahadi da aka kai kan Dahiyeh.

Your Comment

You are replying to: .
captcha